1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar da Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder zai kai kasar China.

Mohammad Nasiru AwalNovember 28, 2003
https://p.dw.com/p/BwWr
A karo na biyar a ran lahadi mai zuwa shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder zai fara wata ziyarar aiki a kasar Sin wato China. Wannan ziyarar dai zata ba shi damar sararawa ta mako daya daga takaddamar da ake yi nan cikin gida game da kasafin kudin Jamus a shekara ta 2004. Ga Jamus dai huldar cinikayya dake tsakaninta da China ita ke kan gaba a dangantakun da ke tsakaninsu, saboda haka tawagar shugaban gwamnati ta kunshi manyan ´yan kasuwa na wannan kasa. A watanni 6 farko na wannan shekara kayayyakin da Jamus ta sayarwa China sun karu da kashi 50 cikin 100, abin da ya sanya China din ta sha gaban kasar Japan a jerin kasashen yankin Asiya da suka fi gudanar da huldar kasuwanci da Jamus. A halin da ake ciki Jamus ta fi sauran kasashen Turai zuba jari a China.
A wannan ziyarar dai bayan ya gana da sabbin mahukuntan birnin Peking shugaban gwamnati tare da tawagarsa zasu halarci bikin baje kolin motoci a birnin Kanton, kafin su yi tattaki zuwa birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan dake kuidu maso yammacin China. Lardin Sichuan dai na kan iyaka da Tibet, kuma yana da yawan mutane da suka kai miliyan 85, kwatankwacin yawan al´umar Jamus. Ziyarar da Schröder zai kai wannan lardi dai karfafa guiwar wani gagarumin shiri ne da gwamnatin China ta fara kimanin shekaru 3 da suka wuce da nufin kyautata halin rayuwar al´umar wannan yanki. Yanzu haka dai an fara aikin gina hanyoyin sadarwa tsakanin yankin na yammacin kasar da kuma yankunan dake gabar teku. Birnin Chengdu na matsayin wata gada tsakanin yammacin da sauran yankunan China, saboda haka kamfanonin Jamus ke kara zuba jari a wannan yanki. Don kwaliya ta biya kudin sabulu, gwamnatin Jamus na shirin bude wani karamin ofishin jakadancinta a birnin na Chengdu.
Ko shakka babu mahukuntan China na maraba da jarurrukan da Jamus ke zubawa a wannan yankin, musamman saboda ganin cewa shirin da gwamnati ke yi na raya wannan yanki na gamuwa da cikas saboda dalilai na karancin kudi. China dai ta fi ko-wace kasa a duniya samun taimakon raya kasa daga Jamus, duk da cewa ba ta cika ka´idojin samun taimakon raya kasa na Jamus saboda take hakin dan Adam da mahukuntan kasar ke yi ba.
A wannan ziyarar dai a karon farko mista Schröder zai gana da sabon FM China Wen Jiabao. Haka zalika an shirya wata ganawar da shugaban kasa Hu Jintao, wanda ya gaji Jiang Zemin. To sai dai bisa ga dukkan alamu ba za´a tabo batun hakin dan Adam a tattaunawar da shugabannin zasu yi ba. Amma ministar shari´a ta Jamus Brigitte Zypries wadda ke cikin tawagar ta Schröder zata tattauna da wakilan gwamnatin China game da batun kare hakkin dan Adam a wannan kasa.