1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Angela Merkel zuwa Rasha a Yau

January 16, 2006
https://p.dw.com/p/BvC4

A yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,zata kai ziyara zuwa kasar Rasha kwanaki uku bayan ziyararta zuwa Amurka,a ci gaba da rangadin aiki na farko zuwa kasashen duniya.

A birnin Moscow ana sa ran zata tattauna da shugaban kasar Rasha Vladmir putin, tare da nufin karfafa dangantaka tsakanin Jamus da Rasha.

Hakazalika zata tattauna rikicin nukiliya na Iran da kuma batun samarda makamashi a nahiyar turai.

Zata kuma tabo batun Chechnya da kuma iko da gwamnatin Rasha take da shi akan kanfanoni masu zaman kansu.

Merkel a ziyarar tata,zata gana da yan adawa na kasar ta Rasha.

Jamiyun siyasa na Jamus dai sun bukaci Merkel da ta tabo batun kare hakkin bil adama a kasar Rasha lokacin wannan ziyara.