1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za ayi zabe a Zimbabuwe a watan Yuli

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 30, 2018

Rahotanni daga kasar Zimbabuwe na nuni da cewa za a gudanar da zabukan kasar a ranar 30 ga watan Yulin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/2ye45
Emmerson Mnangagwa
Shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson MnangagwaHoto: picture-alliance/Photoshot/S.Jusa

 Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya sha alwashin gudanar da sahihin zabe na gaskiya kuma mai inganci. Zaben dai zai kasance zabe na farko tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta a shekara ta 1980 ba tare da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ba, wanda ya sauka cikin watan Nuwamban bara, bayan da fuskanci matsin lamba daga sojoji da ma al'ummar kasar. Ana sa ran Shugaba Mnangagwa ne zai tsaya wa jam'iyya mai mulki ta ZANU-PF yayin da zai fafata da Nelson Chamisa da ke zaman dantakara jam'iyyar adawa ta Movement for Democratic kana shugabanta.