1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara sauraron shari'ar zaben kasar Zimbabuwe

Zulaiha Abubakar
August 22, 2018

Babban alkalin kasar Zimbabuwe ya sanar da ranar Jumma'a mai zuwa a matsayin ranar da zai yanke hukuncin da zai ba shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulkin kasar ko sake sabon zabe.

https://p.dw.com/p/33beQ
Simbabwe Wahlen Nelson Chamisa Anhänger
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Jami'an tsaro dai sun kewaye bangarori daban-daban na Harare babban birnin kasar ta Zimbabuwe cikin shirin ko ta kwana, yayin da kotun zaben ta fara sauraron karar da jam'iyyar adawa ta shigar gabanta, bisa zargin aringizon kuri'a a yayin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Yulin da ya gabata.'Yan adawar dai sun bayyana zaben da cewar yana cike da kura-kurai da kuma magudi a wasu mazabun, tare da neman a sake sabon zabe a kasar. Wannan zabe dai shi ne na farko a kasar bayan da aka tilasta wa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sauka daga kan karagar mulki.