1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: kotu ta kori karar 'yan adawa

Abdullahi Tanko Bala
August 24, 2018

A hukuncin da ta yanke kotun tsarin mulki ta kasar Zimbabuwe ta yi watsi da bukatar 'yan adawa na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar bisa zargin cewa an tafka magudi.

https://p.dw.com/p/33j0c
Simbabwe Wahlkampf Präsident Mnangagwa
Zababben shugaban Zimbabuwe Emerson MnangagwaHoto: Reuters/P. Bulawayo

Kotun tsarin mulki ta kasar Zimbabuwe ta yi watsi da karar da yan adawa suka shigar na neman soke zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yuli bisa zargin an tafka magudi. Alkalan kotun su tara dukkanin su sun amince cewa yan adawar basu bada bayanai da za su gamsar da kotu game da zargin da suka yi ba.


Hukuncin kotun na yau ya tabbatar da nasarar Emerson Mnangagwa a matsayin shugaban kasa.
Wannan ya bashi damar zama shugaba na farko da zai maye gurbin Robert Mugabe da ya shafe shekaru 37 yana mulkin Zimbabuwe. Mnangagwa wanda dan jam'iyyar ZANU-PF ne mai mulki ya sami kashi 50.8 cikin dari na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamaiyarsa Nelson Chamisa na Jam'iyyar MDC ya sami kashi 44.3 cikin dari na kuri'un.


A ranar Lahadi mai zuwa ne za a rantsar da sabon shugaban kasar. Tun da farko an sanya rantsarwar ce a ranar 12 ga wannan watan na Augusta amma aka dage saboda karar da yan adawa suka shigar.