1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zida ya zamo Firaministan Burkina Faso

November 19, 2014

Rahotanni daga kasar Burkina Faso na nuni da cewa an amince da nadin laftanar kanar Isaac Zida a matsayin sabon Firaminsitan gwamnatin rikon kwaryar kasar.

https://p.dw.com/p/1Dplb
Hoto: picture-alliance/dpa/Etienne Kafando

Zida dai shine ya karbi mulki a hannun tsohon shugaban kaar Blaise Compaore, da zanga-zangar nuna adawa da tazarce da 'yan Burkina Faso suka yi, ta tilasta masa yin murabus. Wani babban jami'in gwamnatin kasar ne ya sanar da hakan a yayin da yake karanta wata doka daga shugaban kasar na rikon kwayar Michel Kafando, wanda shima masu ruwa da tsakin suka amince da ya jagoranci kasar nan da shekara guda da za a mika mulki hannun farar hula a kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe