Jawabin Zelensky ga majalisar Jamus
March 17, 2022Talla
Yayin jawabin nasa, shugaba Zelensky ya baiyana wa 'yan majalisar cewa an yi sanya wajen dakatar da yakin da ke gudana tsakanin kasarsa da Rasha.
Cikin kausasan kalamai, shugaba Zelesky ya kalubalanci gwamnatin Jamus kan ci gaba da gudanar da kasuwanci tsakaninta da Rasha yayin da ake tsaka da yakin cacar baki, ya na mai mika bukata ga shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ya rushe wannan katangar. Zelensky ya jadadda cewa zaman lafiya na gaba da kudaden shiga.
Jawabin nasa ta kafar bidiyo na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da ya ke yi na samun goyon bayan shugabannin duniya tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.