Cibiyar Chatham House ta karrama Zelensky
June 29, 2023Talla
Cibiyar Chatham House ta ce shugaban da ke zama tsohon jarumin wasan barkwanci, ya yi nasarar rikidewa zuwa babban dan siyasa kafin daga bisani ya taka muhinmiyar rawa wajen hada kan 'yan kasar Ukraine a lokaci mai tsanani na mamaya daga Rasha.
A shekarar 2005 ne cibiyar Cibiyar Chatham ta fara karrama man'yan mutane da kungiyoyi da suka taka rawar gani a wasu fannoni da suka shafi jagoranci ko aiki. Daga cikin wadanda suka taba lashe kyautar har da tsohon Shugaban kasar Ukraine Viktor Louchtchenko da kuma kungiyar likitocin na gari na kowa wato Medecins Sans Frontieres.