1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya

October 11, 2011

A Talatar nan ce al'ummar Laberiya ke zaɓan sabon shugaban ƙasa da 'yan majaliisar dokokin ƙasar

https://p.dw.com/p/12ptx
Shugaba Ellen Johnson Sirleaf na LaberiyaHoto: DW

A safiyar wannan Talatar ce 'yan Laberiya ke zuwa runfunan kaɗa ƙuri'ar zaɓen sabon shugaban ƙasa. Shugabar ƙasar dake kan mulki a yanzu, wadda ke zama zaɓaɓɓiyar mace ta farkon da ta ɗare kujerar shugabancin wata ƙasa a ɗaukacin nahiyar Afirka, wadda kuma shekarun ta a duniya 72 ne Ellen Johnson Sirleaf, tana fuskantar babban ƙalubale daga Winson Tubman - mai shekaru 70 da haihuwa. Rahotanni suka ce gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan adawar dai ya ƙarfafa ne bayan daya ɗauki tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duniyar nan George Weah a matsayin mai rufa masa baya. A ranar Jumma'ar da ta gabata ce Sirleaf ta sami kyautar zaman lafiya ta Nobel. Baya ga 'yan takarar biyu kuma, akwai wasu 'yan takara 14 da za su fafata tare da su wajen neman muƙamin shugaban ƙasar ta Laberiya. Hakanan 'yan Laberiyar za su zaɓi waɗanda za su wakilce su a majalisar dokokin ƙasar a lokacin wannan zaɓen.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman