1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen raba Sudan

January 7, 2011

Kammala shirye-shiryen gudanar da ƙuri'ar raba gardama a kudancin Sudan

https://p.dw.com/p/zuo2
Shugaban kudancin Sudan Salva KiirHoto: AP

Hukumar da ta shirya ƙuri'ar raba gardama kan 'yancin kan kudancin Sudan da za a yi a ƙarshen mako ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba. Kakakin hukumar George Mater Benjamin ya faɗa a yau Juma'a cewa takardun zaɓe da sauran kayan aiki sun isa a dukkan cibiyoyin zaɓe da a kudancin Sudan ɗin. Shi kuwa tsohon shugaban Amirka Jimmy Carter wanda gidauniyarsa ta Cater Centre Foundation ta girke masu sa ido a zaɓe a faɗin kudancin Sudan ya taya hukumar zaɓen murnar magance manyan matsalolin da ta fuskanta. Shi kuwa Sineta John Kerry kuma masani kan manufofin ƙetare na gwamnati Amirka kira yayi ga Sudan da ta ba da haɗin kai a shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya.

"Muhimmin abu shi ne wanzar da zaman lafiya a waɗannan shirye-shiryen, inda mutane za su yi aiki tare wajen aiwatar da canje-canjen da ake buƙata domin ci-gaban ƙasa."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal