1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen raba gardama a Sudan

January 9, 2011

Shugaban ƙasar Sudan Salva Kiir ya buƙaci al'umar yankin kudancin da su kaɗa Kuri'ar amincewa da mulkin kan yankin

https://p.dw.com/p/zvLi
Masu kaɗa ƙuri'a a runfunan zaɓeHoto: AP

An buɗe runfunan zaɓe a kudancin ƙasar Sudan a zaɓen raba gardama na samar da 'yancin gashin kai ga yankin. Shugaba Salva Kiir wanda ya yi asubancin kada kuri'a ya yi kira ga jama'ar yanki da su tabbatar da ganin an samar da zaman lafiya ta hanyar kaɗa kuri'ar amincewa da samar da yanci. Jim kaɗan bayan ya kaɗa kuri'a, shugaba Salva Kiir ya ce:

"Wannan rana ce dake cike da tarihi da 'yan ƙasar Sudan suke jira ina kira ga jama'a da su yi juriya waɗanda basu samu ba suka kaɗa kuri'a domin kaɗawa.

Sudan Wahlen Kandidat Salva Kiir
Salva Kiir Shugaban Kudancin ƙasar SudanHoto: AP

Masu aiko da rahotannin sun ce duban jama'a sun ja dogon layi a mazaɓu da dama cikin raha da murna. Gabannin zaben dai a jiya an samu ɓarkewar tashin hankali tsakanin yan bindiga na yankin arewaci da sojojin kudancin ƙasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane shidda. Yarjejeniyar samar da zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2005 ita 'ce ta tanadin shirin na yin kuri'a raba gardama wacce kuma ta kawo ƙarshen shekaru 22 na yakin basasa da aka kwashe ana gobzawa a ƙasar.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu