1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen raba-gardama a Masar

March 2, 2011

Hukumomin Masar sun ajiye 19 ga watan Maris a matsayin ranar jefa ƙuri'ar yin na'am ko kuma watsi da tsarin mulkin ƙasar

https://p.dw.com/p/10RlU
Shugaban mulkin sojan Masar Mohamed Hussein TantawiHoto: AP

Gwamnatin mulkin soji a ƙasar Masar ta tsara gudanar da ƙuria'r raba gardama akan samar da sauye-sauye ga tsarin mulkin ƙasar nan da kimanin makonni biyu masu zuwa. Hukumomin sojin dai sun ajiye ranar 19 ga Maris na 2011 ta zama ranar da al'ummar ƙasar za ta amince ko kuma ta yi watsi da sauye-sauyen da ta samar a cikin sabon tsarin mulkin ƙasar, ƙuri'ar da kuma za ta kasance share - fagen zaɓen majalisar dokokin ƙasar na cikin watan Yuni ne - idan Allah ya kaimu, bayan sa kuma a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wani lokaci cikin wannan shekarar da muke ciki. Daga cikin sauye-sauyen dai harda ƙayyade wa'adin shekaru huɗu-huɗu har sau biyu kawai ga shugaban ƙasa. Idan ba'a manta ba dai, hukumomin sojin sun samar da wani kwamiti ne daya yi nazarin irin sauye-sauyen daya kamata a yiwa tsarin mulkin ƙasar - ta yadda za su dace da buƙatun masu zanga-zangar da suka yi nasarar kawar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak a watan Fabrairun daya gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu