1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Majalisar Dokoki zagaye na biyu a Masar

December 5, 2010

Babbar Jamiyyar adawar ƙasar ta Muslim Brotherhood ta janye daga zaɓen bisa zargin hukumar zaɓen da ta keyi da tapka maguɗi.

https://p.dw.com/p/QQ03
Masu zaɓe a MasarHoto: DW

A yau ne al'ummar ƙasar Masar za ta gudanar da zaɓen majalisar dokoki zagaye na biyu, inda ake sa ran Jami'yyar shugaba Hosni Mubarak ta National Demokratic Party za ta lashe kusan dukkan kujerun majalisar.

A yanzu haka dai babbar jamiyyar adawar ƙasar ta 'yan uwa Musulmi, wato Muslim Brotherhood ta janye daga zaɓen bisa zargin da ta ke wa hukumar zaɓen na murɗiya da tabka magudi a zagayen farko. 

Jamiyyar mai mulki ta National Democratic Party ta lashe kujeru 209 daga cikin 221 a zaɓen zagayen farkon da aka gudanar a makon da ya gabata.

Duk da cewa shugaba Mubarak, mai shekaru 82 bai  bayyana ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa ba a zaɓen shekarar 2011, ƙwararru na fasara wannan nasarar da jamiyyar sa ta yi a zagayen farko a matsayin abun da zai faru a zaɓen shugaban ƙasa a baɗi idan Allah ya kai mu.

Jamiyyar ta National Democratic Party dai bata taɓa shan kaye a zaɓen ƙasar ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi