1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

170909 UNESCO Ägypten

September 17, 2009

Ministan Al'adu na Masar na ɗaya daga cikin masu neman matsayin Direktan UNESCO

https://p.dw.com/p/JisF
Hoto: AP

A yau ne ake gudanar da zaɓen babban sakataren hukumar raya al'adu da harkokin ilimi ta Majalisar Ɗunkin Duniya, watau UNESCO a birnin Paris ɗin ƙasar Faransa. Bayan zaɓen na yau dai a tsakiyar watan Oktoba mai kamawa ne zauren majalisar zai tabbatarwa da wanda yayii nasara mukamin.

Ɗan takara daya fi ɗaukar hankalin jama'a da kuma samun mafi yawan goyon baya dai shine ministan harkokin Al'adu na ƙasar Masar Faruk Hosni daga cikin guda tara dake neman wannan kujera. Ya kasance mutumin da yake da goyon baya tsakanin ƙasashen Afirka da na Larabawa da kuma Faransa. Sai dai masu adawa na kanin cewar wasu kalaman musguna da yayi akan Izraela zasu iya jawo masa koma baya.

To sai dai tuni ya nemi afuwa dangane da furucin nasa, amma masu adawa daga kasarsa sunce batazai taɓa samun nasara ba.

Ana dai bayyana Faruk Hosni da kasancewa shararren mutum, wanda a yanzu haka yake kasancewa mai taka rawa wajen haɗewar kasashen yammaci dana gabashi.

"Ya ce na kasance mutumin yankin gabas, wanda ke neman alaka ta musamman tsakanin gabashi da yammaci. Aikina shine sasantawa. A Duniya baki ɗaya ana fuskantar rigingimu da dama, adangane da haka ne ya zamanto wajibi tun daga yanzu mu ceci makomar Duniya"

Ägyptens Kulturminister Faruk Hosni
Farouk HosniHoto: picture-alliance/ dpa

Bugu da kari Minisatan al'adun na Masar Hosni yana muradin gudanar da kamfaign na yaki da sauyin yanayi, talauci da matsalar rashin ilimin karatu da rubutu tsakanin al'umma. Ya yiu alkawarin cigaba da tabbatar da ɗorewar al'adun yahudawa a Masar.

To sai dai tuni Izraela da wasu ƙungiyoyin dake kawance da ita suka fara gudanar da kamfagn na adawa da Faruk Hosni.

A cewar wani marubucin ƙasar ta Masar Alaa al-Aswani, bai kamata kwararre ta fannin zane-zane ya bi ta kowace hannay na ganin cewar ya samu nasara ba. A cewarsa, mutumin daya kasance ministan al'adu na sama da shekaru 20, ba tare da haifar da wani sauyi ba, bai kamata ya a bashi damar matsayin babban Direkta na hukuma kamar UNESCO ba...

"Yace wannan ba filin buga kwallon kafa bane. Inda idan alal misali Jamus ta buga wasa da Masar, ya zamanto wajibi, in marawa tawagar Masar baya. Anan maganace ta a matsayi na na marubuci, dole in bayyana gaskiya da nuna adalaci. a sheakaru huɗu da suka gabata ne, wuta ya ɓarke a babban cibiyar al'adu dake kusa da birnin Alkahira. A harabar cibiyar babu na'urar kashe gobara, sa'annan babu hanyar tsira daga cikin ginin, sanadiyyar haka mutane 50 suka kone har lahira a cikin gobarar. Yaya za ayi mutumin da ya kasa shawo kan gobara a cibiyar al'adu guda ɗaya acikin kasar da yake ministan al'adu, zai iya zama Jagoran UNESCO?"

Der ägyptische Schriftsteller Alaa Al-Aswani
Alaa Al AswanyHoto: picture-alliance/dpa

ana dai ganin cewar babu abunda ya sake cikin shekaru 25 da suka gabata dangane da batutuwa da suka shafi al'adu a Masar.Kuma shin yaya 'yancin zane-zane yake a wannan ƙasa? Ƙwararre ta fannin zane-zane Muhammad Abla ya ɗanɗana yaddad lamarin yake kan zanen batutuwan siyasa..

" Ya ce, akwai iyaka. Alal misali mutum bai isa yayi zanen ɓatanci akan shugaba Mubarak ko kuma ɗansa ba, kamar yadda yake haramtaccen abune ayi zanen Annabi Muhammad tsira da aminci su kara tabbata a gare shi. Ana tantance masu zane-zanen ne da kansu"

Sai dai ana ganin cewar duk da sukan da Faruk Hosni ke fuskanta daga masu adawa, shine ɗan taka daya samu karbuwa, idan aka kwatanta da sauran abokan hamayarsa a neman mukamanin na Direktan UNESCO.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Umaru Aliyu