1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zazzabin dengue ya hallaka mutane a Burkina Faso

October 21, 2023

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Burkina Faso ta sanar da bullar cutar zazzabin dengue. Bullar cutar ta wannan lokacin na zama mafi muni a cikin shekaru.

https://p.dw.com/p/4Xr3X
Nau'in sauron da ke haddasa cutar dengue
Nau'in sauron da ke haddasa cutar dengueHoto: H. Schmidbauer/blickwinkel/picture alliance

Ma'aikatar ta ce ana zargin fiye da mutane 50,000 ne suka kamu da cutar yayin da kimanin 214 suka mutu sanadiyar cutar da ake samu daga sauro a wannan shekarar. An dai samu  bullar cutar ce a babban birnin kasar Ouagadougou da kuma Bobo Dioulasso. Alkalumma sun yi nuni da cewa, cutar zazzabin dengue na kashe mutane a kalla dubu 20 a duk shekara a duniya.

A wannan watan ne dai Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi cutar ka iya zama babbar barazana ga wasu kasashen nahiyar Afirka.