1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 19 sun mutu a Nepal

Binta Aliyu Zurmi
August 16, 2020

Adadain mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar zaftarewar kasa a Nepal ya karu zuwa mutum 19, rundunar yan sandan kasar ce ta sanar da haka bayan da aka yi nasarar zakulo gawarwakin mutum 8 da tabo ya binnesu.

https://p.dw.com/p/3h3Kt
Indien Flut Assam Überflutung
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Nath

Wannan iftila'in dai ya auku ne a kan gwamman mutane da ke wani kauye a yankin arewacin kasar wanda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyar zaftarewar kasar da ta binne mutane da dama tun a ranar Juma'a.

Yanzu haka dai masu aikin ceto na ci gaba da neman wasu mutum 19 da jirage masu saukar ungulu, sai dai ma'aikatan na fatan su kai ga tserartar da mutanen da rayukansu.