1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya na luguden wuta a Nawa

Abdul-raheem Hassan MNA
July 18, 2018

Akalla mutane 12 sun mutu bayan da wasu jiragen yaki suka yi ruwan bama-bamai kan mutane a yankunan da ke hannun 'yan tawaye a lardin Daraa da ke kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/31dLN
Syrien Raketenangriff
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Kungiyar sa ido kan fararen hula ta Syrian Observatory for Human Right mai cibiya a Birtaniya, ta ce sabon samamen da sojojin Siriya suka kai ya ritsa da gidaje da cibiyoyin kiwon lafiya da dama a lardin Daraa, abin da ya sake jefa rayuwar dubban fararen hula da ke gudun hijira a kusa da iyakar Isra'ila.

Hare-hare na baya-bayan nan na zuwa ne bayan da 'yan gudun hijiran Siriya da ke makale a iyakar Isra'ila da Jordan suka koma gidajensu bayan da sojoji suka ayyana kakkabe 'yan tawaye daga birnin.

Birnin Nawa mai kimanin mutane dubu 100 shi ne babban birni da ya rage a hannun 'yan tawayen a lardin Daraa.

Duk da cewa babu tabbacin wadanda ke da alhakin harin kawo yanzu, amma kungiyoyin kare fararen hula na zargin dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan Rasha da jefa rayuwar jama'a a kudancin Siriya cikin kakanikayi.