1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar neman democradiya a Masar

November 22, 2011

Lokacin da Misirawa a watan Fabrairu, suka sami nasarar kayar da gwamnatin Hosni Mubarak ta hanyar zanga-zangar lumana, hakan ya jawo masu goyon baya da amincewa mai yawa daga nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/13EwW
Dubban yan zanga-zanga a dandalin Tahrir na AlkahiraHoto: dapd

A wannan lokaci, yan Masar matasa kwan su da kwarkwatan su, sun fita kan tituna domin zanga-zangar neman yanci da democradiya da kare hakkin su, suka kuma nemi shimfida sabon tsari na mulkin jama'a.

Matasan Masar sun rika amfani da hanyoyin sadarwa na zamani kamar Facebook, wadanda mazauna kasashen tsakiya da gabashin Turai suka yi amfani dasu shekaru da dama da suka wuce a matsayin hanyoyin sadarwa da tuntubar juna kan hanyar kawar da shugabannin su yan kwaminis.

To sai dai Misirawan ba za'a kwatanta su da mazauna nahiyar Turai ba. Kashi 20 cikin dari na yan Masar suna rayuwar su ne cikin hali na talauci, yayin da misalin kashi 40 cikin dari basu iya karatu ko rubutu sosai ba, sa'annan rabin dukkanin matasan kasar masu shekaru tsakanin 20 zuwa 24 basu da aikin yi. Tun daga shekarun baya, bunkasar jama'a da ake samu cikin gaggawa a Masar din ya sanya ana samun karuwar yawan matasa, abin dake nufin ana samun karin rashin jin dadi da rashin gamsuwa, yayin da rashin kwanciyar hankali yake karuwa a wannan kasa, bayan hauhawar farashin kayan masarufi. Ko da shike an sami nasarar kayar da mulkin Mubarak, amma wadanan matsaloli suna nan ba'a magance su ba. Idan aka kwatanta da Masar mazauna nahiyar Turai, har ma misali da na Girka ana iya cewar suna rayuwar su cikin jin dadi da wadata a fannin tattalin arziki.

Ägypten Wahl Wahlen 2011 Feldmarschall Hussein Tantawi
Marshall Mohammed Hussein Tantawi, shugaban majalisar mulkin wucin gadi a MasarHoto: picture alliance/dpa

Halin da ake ciki a Masar ya kuma banbanta da nahiyar Turai a wasu fannoni da dama. Bincike da kafofi dabam dabam suka gudanar ya nuna cewar ana iya samun matsayin da tsarin rayuwa ta addinin musulunci zata kara karfi a kasar, ana iya iya samun gyara ko sake nazarin yarjejeniyar zaman lafiya tareda makwabciyar kasar Israila, kasar da yan Masar tuni suke kyamar ta. Duka wadannan fannoni biyu suna iya zama manufofin aiyukan duk gwamnatin da za'a kafga nan gaba a kasar ta Masar bayan zaben majalisar dokokin da za'a yi a kasar ranar tun daga ranar 28 ga watan Nuwamba, inda ake sa ran cewar jam'iyar nan ta yan uwa musulmi ita ce zata sami nasara.

To sai dai duka wadannan manufofi guda biyu basu dace da bukatun kasashen Turai ba. Duk da haka, akwai wata hukuma a Masar din dake iya hana maida kasar mai bin akidar musulunci. Wannan hukuma kuwa ita ce ta sojan kasar dake kan mulki yanzu, wadanda kuma suke amfani da duka dabarun da suke iyawa domin ci gaba da rike karfin ikon dake hannun su karkashin ko wace gwamnati za'a kafga nan gaba. Sojojin suna iya gabatar da kansu a matsayin wadanda su kadai ne zasu iya tabbatar da zaman lafiya a Masar. Ko da shike hakan yana iya daukar hankalin kasashen yamma, amma tilas a yi taka-tsan-tsan, saboda zaman lafiyar da sojojin suka ce zasu tabatar yana iya rushewa, kamar yadda ya rushe zamanin mulkin Mubarak.

Ägypten Kairo Tahrir Platz Demonstration
Neman democradiya da yancin siyasa a MasarHoto: dapd

Yan Masar da dama suna ganin ba zai yiwu ba, sojoji, wadanda ba zababbun jama'a bane, su kasancve sune wuka, sune nama a game da rubutawa kasar sabon tsarin mulki, yayin da su kansu suke kin bin dokoki da manufofi na democradiya. Wannan ma shi ya sanya yanzui haka, dubban jama'a suke ci gaba da zanga-zanga kan titunan Alkahira da Alexandria da sauran biranen kasar. Mahukuntan na soja dake mulki basa daukar wani mataki na shawokan al'amarin cikin lumana, inda suka gwammace su yi amfani da karfi, abin dake iya jefa Masar cikin mummunan hali na tashin halin hankali.

Gaba daya abin da ake magana a kansa shine: shin Masar zata kai ga samun democradiya na hakika, ko kuwa sojoji zasu ci gaba da rike karfin ikon su a al'amuran kasar. Game da haka, tilas nahiyar Turai ta baiyana goyon baya da taimakon al'ummar Masar a kokarin cimma burin su na tsara siyasar da suke so da kansu a kasar su.