1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar mata a Masar domin adawa da cin zarafin su

December 21, 2011

A dai dai lokacin da mutanan kasar Maser ke kada kuri'unsu a zaban maimaici na 'yan majalisar dokoki, matan kasar sunyi zanga zanga don yin allah wadai da cin zarafin mata da dakarun soji ke yi a kasar.

https://p.dw.com/p/13XNA
Hundreds of Egyptian women march at Cairo streets as they angered by the recent violence used against them in clashes between police and protesters in Cairo, Egypt Tuesday, Dec. 20, 2011. Egypt's ruling generals are coming under mounting criticism at home and abroad for the military's use of excessive force against unarmed protesters, including women, as they try to crush the pro-democracy movement calling for their ouster. Arabic at right read, in Jan. 25, we demand bread, freedom and dignity, and until now we have human rights violations and violence against women. (Foto:Amr Nabil/AP/dapd)
Mata dake bore a MasarHoto: dapd

A dai dai lokacin da mutanan kasar Maser ke kada kuri'unsu a zaban maimaici na 'yan majalisar dokoki, matan kasar sunyi zanga zanga don yin allah wadai da cin zarafin mata da dakarun soji ke yi a kasar.

Zaben da ake gudanar dashi a jihohi tara, a kashi na biyu na zaben kasarda za'a sake karawa tsakanin yan takara fiye da dari biyar da sukai kunnen doki a zaben da ya gabata, na gudana cikin lumana, bayan da hukumar zaben tare da hadin guiwa da jami'an sojin kasar ta kawar da yawancin kura kuran da suka auku a zaben kashi na farko.

Sai dai a wannan karon tashin tashinar da ke ci gaba da faruwa a kasar, ta sanya adadin masu kada kuri'ar yayi kasa. Yadda kungiyoyin matan kasar sukai kira da a fita zanga zangar yin allah wadai da cin zarafin mata da dakarun sojin kasar keyi, yayin gangamin, a wani mataki na karin matsin lamba kan mahukuntan sojin das su gaggauta mika mulki ga farar hula.

Wannan ya zo ne bayan da kafofin watsa labarai sukai ta nuna hotunan dake nuna yadda sojoji ke dukan kawo wuka ga wasu mata da jansu a kasa, kai har ma da yi musu tsirara.

Wannan ya jawo mahukuntan sojin suka fitar da wata takarda wacca cikinta suke neman afuwa wurin yan kasar,musamman ma mata, kan abin da ya faru, suna masu cewa, sojojin da sukai hakan, sunyi gaban kansu ne, kuma za'a hukunta su ba tare da bata lokaci ba.

A daura da haka, matasa masu fafutukar daidaitawa juyin juya halin da akai a kasar sunci gaba da zaman dirshan a dandalin Tahreer, duk da hare hare da suke fuskanta a kai akai, yadda koda a jiya, sai da mutane biyu suka halaka daga cikinsu, abin da ya kai jimallar adadin wadanda suka rigamu gidan gaskiya daga cikinsu ya zuwa mutane gama sha uku, banda wadanda suka jikkata da adadinsu ya dara mutane 500.

In this photo released by Middle East News Agency, the Egyptian official news agency, Kamal el-Ganzoury, Egypt's newly-appointed Prime Minister, speaks to reporters in Cairo, Egypt, Friday, Nov. 25, 2011. Egypt's military rulers picked a prime minister from ousted leader Hosni Mubarak's era to head the next government in a move quickly rejected by tens of thousands of protesters, while the United States ratcheted up pressure on the generals to quickly transfer power to a civilian leadership. Kamal el-Ganzouri, 78, served as prime minister between 1996 and 1999 and was deputy prime minister and planning minister before that. He also was a provincial governor under the late President Anwar Sadat. (AP Photo/Middle East News Agency, HO)
Kamal al-Gansuri Firayim Ministan kasar MasarHoto: AP

Suma jam'iyun siyasa dake ci gaba da kokuwar zabe, sun fitar da wata takarda suna kira ga mahukuntan sojin da su gusa da zaben shugaban kasa zuwa watan biyun sabuwar shekarar dake tafe wato watan Fabrairu,don kashe wutar tashin tashinar siyasa da tsaron da taki ci taki cinyewa.

Su kuwa jami'an tsaron kasar cewa suke suna shirin fitar da sunayen wasu manya a kasar,da ake zargi su da tayar da wutar rikicin baya bayanan daya barke a kasar, wanda ga dukkan alamu yin hakan zai iya sake bude wani sabin babin takaddamar siyasa a kasar ta Masar.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani