1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar dalibai kan muhalli

Zulaiha Abubakar
November 29, 2019

Al'umma a kasar Ostireliya da wasu kasashen Turai sun bi sahun kungiyoyi wajen matsawa shugabanni lamba don lalubo mafita game da matsalolin sauyin yanayi a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake shirin farawa

https://p.dw.com/p/3TyB0
Niederlande Klimaprotest |  Friday Climate Action Day
Hoto: picture-alliance/ANP/V. Jannink

Mai fafutukar kare muhalli daga barazanar sauyin yanayi Greta Thunberg na daga cikin wadanda ke cikin zanga-zangar dalibai a birnin Lisbon na kasar Portugal. Wani jirgin ruwan da ke dauke da Thunberg din ya samu tsaiko a tekun Atlantic sakamakon iska mai karfi kamar yadda ta bayyana wa abokan huldarta a shafukanta na sada zumunta. Zanga-zangar sauyin yanayin a wannan Juma'ar na gudana ne a biranen da yawansu ya kai haura dubu biyu tsakanin kasashe 153 a fadin duniya bisa ga kididdigar da kungiyoyin kare muhalli mai taken Fidays for Future suka fitar.