1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'ar Sudan na son gwamnatin farar hula zalla

Ramatu Garba Baba
December 19, 2021

Masu zanga-zanga sun nemi masu rike da mulki su mika ragamar kasar a hannun gwamnatin farar hula zalla ko su ci gaba da boren da suka kwashi watanni suna yi a kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/44XKP
Sudan | Massenproteste gegen Militärputsch in Omdourman
Hoto: AFP/Getty Images

Da safiyar wannan Lahadi jami'an tsaro suka tsaurara matakan tsaro ta hanyar toshe manyan tituna da gadoji a sassan birnin Khartoum don takawa masu zanga-zangar birki. Sai dai rahotanni na cewa, akasarin gangamin na wannan rana, na tuni ne da cika shekaru uku da soma tattakin da ya kai ga hambarar da tsohuwar gwamnatin tsohon Shugana Omar al-Bashir da kuma dage kan bukatar mika mulki a hannun farar hula.

Gabanin gangamin, a jawabinsa ga 'yan kasa a yammancin ranar Asabar da ta gabata, firaministan kasar Abdallah Hamdok ya yi gargadin cewa juyin-juya halin Sudan yana cikin tsaka mai wuya a sakamakon sabanin ra'ayin siyasa, a lamarin da ya ce, na barazana ga hadin kai da zaman lafiyar kasar.

Tun daga ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata da sojoji suka kwace iko daga hannu Hamdok, kasar ta sake fadawa cikin rudanin siyasa ko da bayan dawo da firaministan mukaminsa da aka yi. Bukatar masu zanga-zangar a yanzu ita ce, mayar da kasar hannu gwamnati mai cikakken mulkin farar hula. Wannan ne karo na tara da al'ummar Sudan ke gudanar da zanga-zangar mai kama da ba-gudu ba ja da baya har sai haka ta cimma ruwa.