1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da gwamnati a Chadi

October 20, 2022

Kwanaki bayan kafa gwamnatin riko a kasar Chadi, kungiyoyin siyasa da na 'yan tawaye sun tayar da kayar baya, suna adawa da majalisar mulki ta soji da aka kara wa wa'adin mulki.

https://p.dw.com/p/4ITjS
Masu zanga-zanga na kone-kone a birnin N'Djamena
Hoto: Le Visionnaire/REUTERS

Dubban ’yan kasar Chadi ne suka amsa kiran shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya wajen fitowa zanga-zangar adawa da gwamnatin rikon kwaryar kasar a wannan Alhamis.

Bayanai na cewa jami’an tsaro sun yi amfani da karfi wajen murkushe zanga-zangar, abin da ya yi sanadin mutuwa da ma jikkatar wasu da dama.

Tun da farko dai masu boren sun lalata motoci da sauran nau’uka na ababen hawa tare ma da farfasa shagunan ‘yan kasuwa abin da ya kara munana lamarin a Chadi.

Yadda jami'an tsaro suka sa masu bore a gaba a birnin N'Djamena
Hoto: Hyacinthe Ndolenodji/REUTERS

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka gudanar da taron kasa domin sama wa Chadi makoma, taron da ya bayanna Shugaba Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasa na riko, shugaban kuma ya nada madugun adawa Saleh Kebzabo a matsayin firaminista.

Wannan lamari bai yi wa wasu kungiyoyin siyasa da na ‘yan tawayen Chadin dadi ba, ganin sun ma kaurace wa taron da aka yi.

Sun kuma nuna kyamarsu karara ga karin wa’adin da aka yi wa majalisar soji na shekaru biyu karkashin jagorancin shugaba na riko Mahamat Idriss Deby Into.

 A ra’ayin ‘yan adawar da ke zanga-zangar, kamata ya yi a bai waw ani shugaba na farar hula ne ba kuma sojojin su ci gaba da mulkin kasar ba.

Chadin dai ta kwashe shekaru masu yawa ba ta ga irin zanga-zangar da aka yi a yau Almahis ba.