Zanga-Zangar ƙasar Masar
February 14, 2011Masu jerin gwanon nuna adawa da gwamnatin daya tilastawa shugaba Hosni Mubarak na Masar yin murabus sun sake komawa dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin al-Qahira, bayan tunda farko sojoji sun umarce su da ficewa daga wurin. Sojojin da suka karɓi ragamar jagoranci a ƙasar ta Masar bayan murabus na Mubarak a ranar Jumma'ar da ta gabata, sun tilastawa rukunin ƙarshe na masu zanga zanga su fice daga dandalin Tahrir, a yayin da rundunar sojin ke ƙoƙarin tabbatar da ikon ta da kuma mayar da bin doka da oda a ƙasar. Kimanin Misirawa 40 ne jami'an 'yan sandan ƙasar suka yiwa ƙawanya a dandalin daya taka rawar da ta kai ga hamɓarar da mulkin shugaba Hosni Mubarak a ranar Jumma'a.
Bayan murabus ɗin ne kuma sojojin suka yi gargaɗi game da duk wani taron jama'a, kana suka haramta duk wani nau'i na yajin aiki. A cikin wata sanarwar da rundunar sojin ta fitar a jiya Lahadi, ta ambata Muhammad Husseini Tantawi a matsayin wanda zai shugabanci majalisar sojin da za ta kula da lamuran ƙasar - har na tsawon watanni shidda ko kuma har bayan gudanar da zaɓukan majalisar dokoki da kuma na shugaban ƙasa.
A halin da ake ciki kuma, firaministan ƙasar ta Masar Ahmad Schafik ya tabbatar da cewar, shugaba Mubarak na ci gaba da gudanar da harkokin sa ne a wurin shaƙatawar nan na Sharm el-Sheikh:
" Shugaba Mubarak dai a yanzun nan da nake magana da kai yana Sharm el-Sheikh. Har dai ya zuwa wannan safiyar, abinda na sani kenan, kuma na yi amannar har yanzu yana can."
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal