1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ta yi ƙamari a Siriya

March 27, 2011

Masu zanga-zangar neman sauyi a Siriya sun saka shugaba Bachar al-Assad cikin tsaka mai wuya

https://p.dw.com/p/10iCC
Bashar al AssadHoto: AP

A ƙasar Siriya an ci gaba da zanga zanga duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro su ka yi na tarwatsa masu boren adawa da gwamnati. Masu zanga zangar sun ƙona ofishin jam'iyyar da ke mulkin ƙasar ta Baath a birnin Latakiya mai tashar jiragen ruwa. An bada sanarwar kashe mutane biyu da raunana wasu biyun. Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty ta ce kama daga shekaran jiya an kashe aƙalla mutane 50 a ƙasar ta Siriya,tare da tsafke mutane 200 daga cikinsu. Rahotannin sun nunar da cewa mutane dubu huɗu ne su ka gudanar zanga-zanga a birnin Douma kusa da Damascus, domin tilasawa gwamnati Bashar Al Assad aiwatar da sauye-sauye ciki kuwa har da na siyasa. Kamfanin dillacin labaran Reuters ya nunar da cewa jami'an tsaro sun buɗe wuta lokacin da masu zanga-zangar suka jefi butunbutumin tsohon shugaban ƙasar Siriya wato Hafez al Assad. A birnin Sanamaein kuwa, mutane 20 suka rigamu gidan gaskiya lokacin da sojojin suka yi harbe harben kan mai uwa da wabi akan gungun masu zanga-zanga.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi