1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Zanga-Zanga ta hana jirage tashi

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2024

Sama da jirage 100 masu zanga-zangar rajin kare muhalli suka tilasta aka soke tashinsu, a filin jiragen sama na birnin Frankfurt da ke zaman mafi yawan hada-hadar jiragen sama a Jamus.

https://p.dw.com/p/4ijVz
Jamus | Frankfurt | Jiragen Sama < Tsaiko | Zanga-zanga | Muhalli
'Yan rajin kare muhalli sun hana jirage tashi a FrankfurtHoto: picture alliance/dpa/TNN

Dubban masu rajin kare muhallin sun tsara gudanar da zanga-zanga a kasashen Turai baki daya, domin dakile zirga-zirgar jiragen sama a daidai lokacin da mutane da dama ke tafiya hutun bazara  da nufin nuna illa da barazanar sauyi ko dumamar yanayi. Rahotanni daga filin jiragen saman na Frankfurt sun nunar da cewa masu zanga-zangar sun karya shingen jami'an tsaro tare da kustsa kansu kan titunan jiragen saman, abin da ya tilsta 'yan sanda da jami'an kashe gobara da sauran jami'an tsaron filin jiragen saman daukar mataki. Masu zanga-zangar dai sun tilasta soke tashin kimanin jiragen sama 140, kuma kawo yanzu babu wani karin bayani kan sabon lokacin da aka  tsara tashinsu saboda fargabar sake samun kutsen 'yan rajin kare muhallin.