1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga: Shugaba Buhari ya ce an kashe mutane

October 24, 2020

Bayan kwashe kwanaki, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tabbatar da mutuwar fararen hula 51 sanadiyyar zanga-zangar kwanakin da suka gabata a wasu sassan kasar.

https://p.dw.com/p/3kNUt
Nigeria Abuja | End Sars Proteste | Demonstranten
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Shugaba Buhari wanda bai amince cewar jami'an tsaro sun kashe mutane a lamarin ba, ya ce masu zanga-zanga da ta koma tarzoma sun kashe 'yan sanda 11 da ma wasu jami'an soja bakwai, abin da ya kai adadin 69 ke nan da suka salwanta.

Zanga-zangar da ta samo asali daga kin jinin 'yan sandan SARS da ake zargi da zalunci da kashe-kashe, ta koma hannun bata-gari da suka yi ta kone-konen ma'aikatun gwamnati da wuraren kasuwanci a kasar.

A lokacin da yake yi wa tsoffin shugabannin kasar jawabi a jiya Juma'a, Shugaba Buhari ya ce jami'an tsaro sun yi kokarinsu wajen kamewa da kai zuciya nesa lokacin tarzomar.