1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren kin jinin dokar zama dan kasa ta kankama a Indiya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 19, 2019

Duban jama'a sun fito domnin ci gaba da nuna adawa da dokar nan ta zama dan kasa da majalisar dokokin kasar Indiya ta yi na'am da ita da ke ci gaba da haifar da tarnaki.

https://p.dw.com/p/3V5nn
Indien Proteste gegen neues  Einbürgerungsgesetz
Hoto: Reuters/D. Sissiqui

Masu bore da zanga-zanga sun yi  dauki ba dadi da jami'an tsaro wasu sassan kasar da dama musamman ma a birnin New Delhi da sauran jihohin da ke arewacin kasar, kana tuni jihohin suka kirkoro dokokin da ke hana duk wani taro na jama'a da suka wuce mutun hudu. Tuni hukumomin kasar suka dauki matakin toshe duk wasu kafafe na sadarwa irin na zamani a yankunan da ake fama da zanga-zangar ciki har da wasu wurare a birnin Delh. Masu aiko da rahotanni sun ce an hallaka mutane da dama a yayin zanga zangar wacce ta doshe mako daya.