Zanga Zanga a ƙasar Masar
May 4, 2012Masu zanga zangar sun riƙa jifar yan sanda da duwarwatsu su kuma suna harba masu tiya gaz tare da yin amfani da mesa da ke yin feshin ruwa zafi.Waɗanda suka ganewa idanun su sun ce sojojin da aka jibge a gewayen ofishin ministan tsaro inda a makon jiya wani tashin hankali da ya ɓarke ya yi sanadiyar mutuwar mutane guda 11.
Sun sha suka daga masu zanga zangar da ke buƙatar saukar Marchel Tantaoui daga mulki.Wani babban habsan sojin ya ce jama'ar suna ɗauke da miyagun makamai sannan ya gargaɗe su da su yi sasauci.''ya ce muna bayan al'ummar ƙasar Masar kammar tun lokacin da aka fara yin zanga zanga ta ƙemar Hosni Moubarak ya ce kuma mun yi alƙawarin ba za mu yi amfani da karfin bindiga ba domin murkushe jama'ar
An dai tsara za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar a ranaku 23 da 24 ga wannan wata.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar