1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar Girka

February 8, 2012

Duban jama'a sun yin allah wadai da sauye sauye da gwamnatin ta ke shirin ƙadamarwa

https://p.dw.com/p/13z3R
Riot Police push back protestors, one waving the Greek flag, who try to enter at the Parliament building at Athens' main Syntagma square, during a 24-hour strike on Tuesday, Feb. 7, 2012. A general strike against the impending cutbacks stopped train and ferry services nationwide, while many schools and banks were closed and state hospitals worked on skeleton staff. (Foto:Petros Giannakouris/AP/dapd)
Masu zanga zangaHoto: AP

Masu aiko da rahotannin sun ce an sha arangama tsakanin masu bore da suka bazu akan tituna a birnin Athens da kuma jami'an tsaro waɗanda suka yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama'ar.

Lamarin dai ya biyo bayan taron shawarwarin da aka soma tsakanin gwamnatin ta Girka da man'yan hukumomi na kuɗi na duniya akan sauyen sauyen da suka tilasawa gwamnatin gabannin samun wani ƙarin tallafin na kuɗaɗe kimanin biliyan dubu 130 na Euro.Sharuɗan dai da hukumomin kuɗin da na ƙungiyar Tarrayar Turai suka gabatar ga ƙasar ta Girka sun tanadi matakan rage ma'aikata, da kuɗaɗen da gwamnatin take kashewa da kuma ƙara kuɗaden haraji.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu