Zanga-zanga a Pakistan
November 5, 2007Talla
Jama´ar ƙasar Pakistan, da ma ƙasashe da dama na dunia, na ci gaba da yin Allah wadai ga dokar ta ɓacen da shugaba Jannar Pervez Musharaf ya girka a ƙasar Pakistan.
A biranen Rawalpindi da Karachi a yau ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta shirya zanga-zanga, domin nuna adawa da wannan doka, saidai jami´an tsaro sun yi anfani da ƙarfin tuwa domin tarwasta zanga-zangar.
Ya zuwa yanzu rahottani daga Pakistan sun ce jami´an tsaron sun cafke a ƙalla lauyoyi 50.
A nasu ɓangare yan adawar ƙasar Pakistan sun ci alwashin shirya tasu zanga-zangar, duk kuwa da kashedin da gwamnati ta yayi masu.
A wani mataki na cilastawa Pervez Musharaf ya lashe amen sa, ƙasar Amurka ta yi barazanar dakatar da tattanawar da ta ke da Pakistan.