1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Masar

November 18, 2011

Masu bore sun sake komawa dandalin Tahrir a birnin Alkahira don kira ga Majalisar sojin rikon kwaryar kasar da ta mikawa fararen hula mulki

https://p.dw.com/p/13D71
Hoto: dapd

Dubun dubatan masu zanga-zanga a Masar suka koma dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira a wani gagarumin jerin gwano a wani mataki na neman shugabanin mulkin sojin kasar da suka mika madafun iko bayan kadawar guguwar neman sauyin da ya hambarar da mulkin tsohon shugaba Hosni Mubarak. A yayin da zaben kasar na farko tun bayan kadawar guguwar sauyin ke karatowa masu boren na neman sake samun karfin fada a ji a kan kundin tsarin mulkin da a yanzu haka majalisar dokokin kasar ke kwaskware daftarin. An dai gudanar da zanga-zangar ta wannan juma'a ce a karkashin jagorancin kungiyar 'yan uwa musulmi da sauran kungiyoyin siyasa wadanda suka ra'ayinsu ya zo daya a kan cewa lokaci yayi da ya kamata majalisar rikon kwaryar sojin ta mikawa fararen hula mulki. Haka nan kuma masu adawan sun nuna bacin ransu da yadda majalisar sojin ta baiwa kanta ikon zama matakin karshe a kan kowace irin shawara da za'a yanke a kasar. A ran 28 ga wannan wata na Nuwamba ake sa ran gudanar da zaben 'yan Majalisar dokoki.

Mawalafiya: Pinado Abdu

Edita: Usman Shehu Usman