1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Libiya

February 16, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) ta buƙaci gwamnatin Libiya da ta tabbatar da 'yancin faɗin albarkacin baki bayan aukuwar zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/10I1b
Babban dandalin birnin BenghaziHoto: picture alliance/Lonely Planet Images

A matsayin martaninta ga gumurzun da aka samu a ranar Talata da dare a birnin Benghazi da ke arewacin ƙasar Libiya, Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga mahukuntan ƙasar da su tabbatar da 'yancin faɗin albarkacin baki. Gidan telebijan gwamanatin ƙasar ta Libiya ya ce kimanin mutane ɗari biyar ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin gwamnati domin yin kira da a saki jami'an kare haƙƙin bil Adama. Daga nan ne kuma suka zarce zuwa wani babban dandali da ke birnin na Benghazi inda suka yi gumurzu da 'yan sanda da masu goyon bayan gwamnati . Shugaban asibitin wannan wuri ya ce mutane 38 cikinsu har da 'yan sanda ne aka duba sakamakon raunkan da suka samu yayin arangamar.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu