1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a kasar Girka

October 19, 2011

Ƙungiyoyin kwadago da al'umma Girka na nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati da zai sallami duban ma'aikata gwamnati

https://p.dw.com/p/12vNL
Masu gudanar da zanga zangaHoto: dapd

'Yan 'sanda a birnin Athens na ƙasar Girka  sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajan tarwatsa wasu matasan da suka rufe fuskokinsu da riguna masu huluna .A gangami da sama da mutane dubu 100 suka gudanar domin nuna rashin amince wa da matakin tsuke bakin aljihu da gwamnatin ta dauka ''wani ɗan ƙasar kenan ya na mai cewa sakamakon wannan shiri na gwamnatin ma'aikata da dama ne zasu rasa aiki, ya ce ga kuma wahalolin rayuwa.

A halin da ake ciki dai makarantu da bankuna da ofisoshin gwamnati da kuma al 'amuran sufuri sun tsaya cik a sakamakon yajin aiki na kwanaki biyu. Nan gaba ne dai majalisar dokoki ta ƙasar ta Girka za ta kaɗa ƙuri'a akan shirin tsuke bakin aljihu wanda ƙasar ta cimmawa tare da kungiyar Tarrayar Turai da kuma hukumomin lamuni na duniya;shirin  ya tanadi rage  kuɗaɗen albashin ma'aikata da rage kuɗaɗen fansho da kuma kara yawan haraji tare da rage yawan ma'aikatan gwamnati .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita       : Zainab Mohammed Abubakar