1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Afrika ta Kudu

October 13, 2012

Jami'an 'yan sanda a Afrika ta Kudu sun yi taho mu gama da wasu ma'aikatan haƙar ma'adanai yayin wata zanga-zanga da su ka yi a Rustenburg da ke Johannesburg.

https://p.dw.com/p/16PfB
Hoto: AFP/Getty Images

'Yan sandan sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zangar inda su kuma su ka mai da martani da kwalabe da ke cike da fetur wanda su ka kunna wa wuta, lamarin da ya jawo lalacewar motocin 'yan sandan. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yankin na Rustenburg ya tabbatar da faruwar tashin-tashinar inda ya ƙara da cewa arangamar ba ta yi sanadiyyar rasa rai ko jikkata ba.

Ma'aiktan dai sun gudanar da zanga-zanagr ce da nufin nuna fushinsu game da batun rashin inganta yanayin aiki da kuma ƙarin albashi kuma kamar yadda Evans Ramokga daya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, za su cigaba da zanga-zangar har sai an biya mu su buƙataunsu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas