1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga Zanga a ƙasar Masar

May 4, 2012

An sha mumunar artabu tsakanin yan sanda da masu yin bore a tsakiyar birnin Alƙahira

https://p.dw.com/p/14qL5
epa03203709 An Egyptian anti-riot soldier (C) gestures towards anti-military protesters during clashes at Abbassiya square, Cairo, Egypt, 02 May 2012. Media reports quoting medical sources state that at least nine people were killed in clashes between anti-military protesters and unknown attackers near the Defence Ministry in Cairo. Dozens of people were also injured in the clashes, which erupted when the assailants, whom the opposition called pro-government thugs, cracked down on the protesters. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Masu zanga zangar sun riƙa jifar yan sanda da duwarwatsu su kuma suna harba masu tiya gaz tare da yin amfani da mesa da ke yin feshin ruwa zafi.Waɗanda suka ganewa idanun su sun ce sojojin da aka jibge a gewayen ofishin ministan tsaro inda a makon jiya wani tashin hankali da ya ɓarke ya yi sanadiyar mutuwar mutane guda 11.

Sun sha suka daga masu zanga zangar da ke buƙatar saukar Marchel Tantaoui daga mulki.Wani babban habsan sojin ya ce jama'ar suna ɗauke da miyagun makamai sannan ya gargaɗe su da su yi sasauci.''ya ce muna bayan al'ummar ƙasar Masar kammar tun lokacin da aka fara yin zanga zanga ta ƙemar Hosni Moubarak ya ce kuma mun yi alƙawarin ba za mu yi amfani da karfin bindiga ba domin murkushe jama'ar

An dai tsara za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar a ranaku 23 da 24 ga wannan wata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar