1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar Masar

November 20, 2011

Jama'ar na neman gwamnatin ta soke wasu sauye sauye da ta ƙaddamar akan harkokin soji

https://p.dw.com/p/13Dpb
Yan' sanda suna karawa da masu zanga zanga a dandalin TahrirHoto: dapd

An bada rahoton cewa mutane biyu suka mutu a birnin Alƙahira na ƙasar Masar a daran asabar zuwa lahadi a sakamakon arangamar da aka sha tsakanin yanä' sanda da masu gudanar zanga da suka riƙa jiffa da duwarwatsu ga jami'an tsaron.An dai fara karawa ne tsakanin sasan biyu tun sa'ilin da yan' sandar suka yi kokarin tarwatsa masu yin boren da suka yi dandanzo a dandalin Tahriri. A cikin wata sanarwa da ofishin ministan cikin gidan ya baiyana; ta ce jami'an tsaron sun yi harbi da harsahen roba sanan kuma tare da sauran makaman da doka ta amice da su.

wannan al 'ammari dai ya zone a daidai lokacin da ya rage ƙwanaki goma a gudanar da zaɓen yan majalisun dokoki tun bayan faduwar gwamntin Hosni Moubarak.Mataimakin fraministan ƙasar ne dai ya gabatar da wata doka ta yi gyaran fuskan ga al'amuran soji na ƙasar wanda al'ummar ta ce ba ta yarda da su ba.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu