Zanga zanga a ƙasar Faransa
August 28, 2010Ƙungiyoyin kare haƙƙin bi adama a ƙasar Faransa sun gudanar da zanga zangar nuna goyon baya ga Sakineh Mohammadi Ashtiani wata 'yar ƙasar Iran da ke fuskantar hukuncin kisa ta hanyar jefewa , bayan da aka sameta da laifin yin zina da kuma bada haɗin kai wajan aikata kisa akan mai gidanta
Zanga zangar wacce ta samu hallarta kimani mutane 300 a birnin Paris na ƙasar ta Faransa masu aiko da rahotanin sun ce haka kuma an gudanar da irinta a cikin wasu garuruwa guda 100 na duniya a lokaci ɗaya.
Sakineh Ashtiani mai shekaru 43 da haifuwa an yanke mata hukuncin rajamu ne tun a shekara ta 2006 ,to amma daga bisanin hukumomin na ƙasar ta Iran sun bada sanarwa ɗage hukumci kafin yanke shawara ta ƙarshe.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala