1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma zaman shari'ar Kambwili a Lusaka

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2018

Wata kotun birnin Lusaka ta soma zaman shari'ar Chishimba Kambwili dan siyasar da ya yi fice wajen caccakar shugaban kasar Edgar Lungu da ake zargi da tara dukiyar haram.

https://p.dw.com/p/2zmga
FALSCHE BESCHREIBUNG - Sambia Lusaka Wahlen Präsident Edgar Lungu bei Stimmabgabe
Hoto: Getty Images/AFP/G. Guercia

A kasar Zambiya wata kotun birnin Luzaka ta fara a wannan Litinin zaman shari'ar Chishimba Kambwili dan siyasar nan da ya yi kaurin suna wajen caccakar shugaban kasar Edgar Lungu. A watan Maris din da ya gabata ne dai aka kama Mista Kambwili a gidansa da ke a birnin Lusaka a bisa zargin aikata wasu laifuka har 39 da suka hada da na mallakar wasu gidaje ta hanyar amfani da wasu kudaden da ya samo ta haramtacciyar hanya. 

Sai dai kuma da yake kare kansa a wannan Litinin a gaban kuliya dan siyasar mai shekaru 48 wanda kuma dan majalisa ne daga jam'iyya mai mulki ta Front Patriotique ya yi watsi da illahirin zarge-zargen da ake yi masa yana mai cewa a shirye yake ya kawo hujjoji na halittattun hanyoyin da ya bi wajen samun wadannan kudade nasa.