1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na zaman makoki

Ramatu Garba Baba
August 18, 2021

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta aiyana zaman makoki na kwanaki biyu daga wannan Laraba don nuna alhini kan kisan gillan da aka yi wa wasu fararen hula sama da 30.

https://p.dw.com/p/3z7yI
Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Gwamnatin Nijar ta bayar da umarnin sauko da tutar kasa a duk sassan kasar a yayin da ta sha alwashin ci gaba da yakar ayyukan ta'addanci har sai ta kai ga cimma nasara.

Yankin da aka kai harin dama na fama da ayyukan mayakan Al-Qaeda da IS, sai dai kuma harin na kauyen Dare-Day da ke jahar Tillabery, ya tayar da hankula da jefa jama'a cikin fargaba, ganin yadda maharan da suka kai hari kan manoma, a wannan karon suka hada da mata da kuma kananan yara. 

A wani rahoto da Kungiyar Human Rights Watch ta fitar a makon jiya, ta ce, fararen hula sama da 420 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hare-haren mayakan da ke da'awar jihadi a jahar ta Tillabery.