1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dar-dar a kasar Togo

Ramatu Garba Baba
October 18, 2017

Jami’an tsaron a kasar Togo sun yi anfani da karfi don tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi facali da umarnin gwamnati na kaucewa duk wani taro da sunan adawa da mulkin shugaba Faure Gnassingbe.

https://p.dw.com/p/2m7Vg
Togo Protest gegen die Regierung
Hoto: picture alliance/dpa/abaca/A. Logo

An samu barkewar rikici a yayin da 'yan sanda da sojoji suka yi kokarin tarwatsa dandazon mutanen da suka amsa kiran da jam'iyyun adawa suka yi na nuna rashin amincewa da gwamnati mai ci, rahotani na cewa mutane da dama sun sami rauni a sanadiyar arangama a tsakanin jami'an tsaro da masu boren, al'amura sun tsaya cak a Lome babban birnin kasar dama wasu garuruwan da aka gudanar da zanga zangar bayan da kura ta lafa.

Tun a watan Augustar da ta gabata ne Jam'iyar adawa ta sanar cewa za ta gudanar da zanga zanga ta kwanaki biyu don ganin gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe ta yi gyara don tsayar da wa'adin mulkin shugaban kasa zuwa biyu kacal tare da ganin shugaban ya sauka daga mulkin kasar da ya shafe fiye da shekaru goma yana yi. A shekarar 2005 daruruwan mutane sun rasa rayukansu a yayin zaben da ya bai wa shugaban nasara.