1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Zafin rana ya ta'azzara a Turai

Gazali Abdou Tasawa
August 4, 2018

Yanayin zafi na kara ta'azzara a kasashen Turai inda yanzu haka hankalin jama'a ke ci gaba da tashi dangane da illar da matsalar ke haddasawa ga lafiyar jama'a da ma a harakokin noma.

https://p.dw.com/p/32c62
Deutschland Hitzewelle
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Yanzu haka dai ko a wannan mako zafin ranar ya halaka mutane uku a kasar Spain inda a wasu yankunan yanayin zafi ya kai murabbadin digirin 44 a ma'aunin zafi na Celcius. 

A kasar Potugal yanayin zafin ya zarce digiri 45 a garin Alvega. Hukumar yanayi ta kasar dai ta ayyana dokar ta bace a wasu jihohi 11 na kasar a ranaikun yau Asabar da gobe Lahadi inda zafin ka iya kai koluluwar da ba taba fuskanta ba a tarihin kasar ta Potugal. 

Kasar Sweden ma wacce ga al'ada ke da yanayin sanhin kusan a kowani lokaci na shekara ta fuskanci a karshen watan Yulin da ya gabata zafin da y kai na digiri 30 wanda ke zama mafi tsanani a shekaru 250 na baya bayan nan a kasar. Lamarin da ya soma yin tasiri ga harakokin noma da kafewar tabkuna da koguna da kuma tashin gobarar daji a kasashen na Turai da dama.  

A kasashen Turan da dama dubunnan jam'a ne ke yi cincirindo a gabobin teku, koguna da tabkuna, a yayin da a birane da dama mahukunta suka tanadi fanfuna masu feshin ruwa inda jama'a ke zuwa suna rage radadin zafin ranar.