1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda: Zabtarewar kasa ta kashe mutum 34

Ramatu Garba Baba
October 12, 2018

Hukumomin kasar Yuganda sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 34 a sakamakon iftla'in zabtarewar kasa da ta afka wa gabashin kasar, ana kuma fargabar alkaluman su zarta haka ganin munin lamarin.

https://p.dw.com/p/36PcQ
Erdrutsch Äthiopien Oromia Region West Arsi Zone
Hoto: West Arsi Zone Government Communication Affairs Office

Zabtarewar lakar a sanadiyar mamakon ruwan sama ta binne tarin gidaje da kuma dabbobi, akwai kuma mutane da yawa da ba a ji duriyarsu ba tun faruwar lamarin. Hukumomi sun bazama aikin ceto rayuka tare da tallafawa wadanda suka tsira da rayukansu. Yankin na gabashin kasar Yugandan da ke kan iyaka da kasar Kenya ya sha fama da wannan matsala a shekarun baya.