1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe mai cike da fatan samun sauyi a Kuwaiti

Zainab Mohammed Abubakar
December 5, 2020

Cike da fatan samun sauyi ne al'ummar Kuwaiti suka yi fitar farin dango a zaben 'yan majalisar wakilan kasar, inda aka dauki matakan kariya saboda annobar COVID 19.

https://p.dw.com/p/3mHIX
Kuwait Parlamentswahlen 2016
Hoto: picture-alliance/AA/J. Abdulkhaleg

Masarautar mai arzikin mai ta kasance daya tilo da ta kafa wasu dokoki masu tsauri a yankin na Gulf na yaki da corona, wadda kuma ta aiwatar da dokar kulle na tsawon watanni a farkon wannan shekarar.

A yayin da ak sassauta wasu dokokin, an haramta taron yakin neman zabe gabanin ranar ta yau, a yayin da aka wajabta wa jama'a sanya takunkumi da zarar sun fita dga gidajensu daura da duba yanayin zafin jiki.

A wannan Asabar din dai an tilasta amfani da safar hannu ga masu kada kuri'u a dukkan cibiyoyin zabe 102 da ke fadin masarautar ta Kuwaiti.