1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya: Sakamakon zabe mai abin mamaki

Uwais Abubakar Idris MA
February 26, 2019

A Najeriya sakamakon zabe daga jihohi a tsakanin manyan 'yan takarar shugaban kasa da ke ci gaba da shigowa na fitowa ne ta yadda ba a zato.

https://p.dw.com/p/3E7SZ
Manyan 'yan takaran Najeriya, Buhari da Atiku
Manyan 'yan takaran Najeriya, Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar

Sakamakon zaben na shugaban Najeriya na nuna ban mamaki a jihohi da dama da bisa al’ada ake sa ran wani dan takara zai bada mamaki amma sai ya tsira da kyar ko kuma su yi kankankan a tsakanin ‘yan takarar biyu Shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar ya lashe jiharsa ta Adamawa duk da cewa tana karkashin jam’iyyar APC, domin ita ce kadai jihar ta ya lashe a yankin da ya fito, a daya bangaren kuri’un da jam’iyyar APC ta yi kusan kunnen doki ne a jihohin kudu maso yammacin Najeriya duk da karfin da ake ganin jam’iyyar APC na da shi.

A jihar Lagos da yawan kuri’u 132 jam’iyyar APC ta wuce PDP, haka al’amarin yake a galibin jihohin yankin inda PDP ce ma ta lashe zaben jihar Oyo jihar da APC ce ke mulki

Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon jihohi 24 ne daga cikin jihohi 36 da Abuja na Najeriyar, abin da ke nuna aiki ya yi nisa na bayyana sakamakon zaben.

A bisa kiyasin kuri’u da ake da su a yanzu, ya nuna cewa jam’iyyar APC na da fiye da kuri’u milyan 8 da dubu 570, sai jam’iyyar PDP da ke da  fiye da kuri’u milyan 6 da dubu 969. 

A yayinda ‘yan Najeriya ke ci gaba da jiran samun kammalallen sakamakon zaben, ana ci gaba da kiran amincewa da shi don samun zaman lafiya da dorewar dimukuradiyyar kasar.