1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Majalisar dokoki a Masar

November 28, 2011

Masu sanya ido zaben Masar sun ce duk da cewa kurar masu zanga-zanga ya dan lafa, har yanzu akwai fargabar rashin tsaro

https://p.dw.com/p/13IWH
Wasu Misrawa mata suna layin jefa kuri'aHoto: dapd

Alummar Masar na nan na jefa kuri'a a wannan litinin, abun da aka kira zabe mafi sahihanci a kasar, a daidai lokacin da yan kasar ke cigaba da nuna adawa mulkin sojin da ke rike da madafun iko. Wannan ne kuma karo na farko da kasar ke gudanar da zaben majalisar dokoki tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a watan fabrairun da ya gabata.

A matakin farko na zaben mazauna biranen Alkahira da Iskandariya da wasu larduna bakwai zasu jefa kuri'un su kana kuma a watannin Disemba da Janairu wasu larduna 18 suma zasu bi sahu.

Dama dai an gudanar da yakin neman zaben cikin wani yanayi na zanga-zanga, amma duk da wannan hargitsi majalisar koli na mulkin sojin kasar ta hakikance a kan gudanar da zaben na yau. Jamiyyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da kuma sabbin jamiyyun masu tsatsaurar ra'ayin Islama su ma sun goyi bayan gudanar da zaben. Kawo yanzu dai ba'a sami rahotannin tarzoma ba a yawancin yankunan da aka fara gudanar zaben, to sai dai ra'ayoyi sun banbanta a dandalin Tahrir dangane da wanda ya kamata a zaba a yayin da wasu kuma suke cewa zasu yi rowan kuri'unsu Heba Morayef jami'a ce a kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch wadda take sanya ido a kan yadda zaben ke gudana a alkahira

"Akwai matukar damuwa bisa sha'anin tsaro to amma yanzu dai kura ta soma lafawa dangane da gudanar da zaben"

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita:            Halima Balaraba Abbas