1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya barazanar tashin hankali

Binta Aliyu Zurmi SB
December 19, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da yadda ake shirin zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3mxoQ
Zentralafrikanische Republik Wahlkampf 2020
Hoto: Camille Laffont/APF/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin da ke neman tayar da husuma da su kai zuciya nesa a yayin da ake daf da tunkarar manyan zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya soki yadda wasu kungiyoyin sa kai uku suka bayyana anniyarsu ta yin fito na fito da gwamnati mai ci yanzu, muddin ta shirya magudi, kuma ta lashe zaben shugaban kasar na ranar 27 ga wannan watan.

Yanzu hakan dai an baza dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya cikin fadin kasar domin dakile duk wata fitina da ka iya kawo illa ga zaben kasar.