1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan takara uku kawai za su fafata a zaben Benin

April 9, 2021

A ranar Lahadi za a gudanar da zaben shugaban kasa a jamhuriyar Benin, inda mutum uku kacal za su tsaya takara. Dalilin haka shi ne wani tsarin tantance 'yan takara da tun farko ya yi waje road da sanannun 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/3rmv4
Benin Wahlen Wähler
Hoto: Séraphin Zounyekpe

Benin a cikin yakin neman zabe. A Cotonou cibiyar hada-hadar kasuwanci mai kuma mazauna dubu 800, a kulum ana lika kwalaye da ke nuni da zaben shugaban kasa na ranar 11 ga watan nan na Afrilu. Sai dai mutane biyu suka mamaye kamfen din wato Shugaban kasa Patrice Talon da matamakiyarsa Mariam Chabi Talata, wadda idan shugaban ya yi nasara, za ta zama mataimakiyar shugaban kasa.

Babu sanannun 'yan takara da za su yi karon batan karfe da Patrice Talon a zaben shugaban kasa

Benin Wahlen Wähler
Hoto: Séraphin Zounyekpe

Flora Agoudavi daya ce a cikik magoya bayan shugaba Talon ce.Ta ce: "Ba zan bari a bar ni a baya ba a gun yakin neman zaben shugaban kasa. Zan ba shi kuri'a ta, saboda da shi na zo nan wurin. Muna bukatar canji musamman na walwalar jama'a. Mu mata muna son a saukaka mana hanyar samun kananan basussuka. Dole ne ya kula da wannan idan aka sake zabensa."

Shugaba Talon ya so daidaita komai cikin wa'adin mulkinsa na farko na shekaru biyar. Bayan zabensa a 2016 ya sanar da kawo sauyi, ba kuma zai sake yin takara ba. Sai dai bai cika akawari ba, maimakon haka cewa yake dole ne a kammala aikin da aka fara. Sabanin zabukan shugaban kasa da suka gabata, yanzu an rage yawan 'yan takara zuwa mutum uku, bayan Shugaba Talon, akwai Corentin Kohoue da Alassane Soumanou wadanda dukkansu biyu ba sanannu ba ne a wajen masu zabe.

Wani sabon tsarin zabe ya takaita yawan 'yan takara a zaben na Benin
 
Wani sabon tsari zabe da aka kirkiro a 2019 ya takaita yawan 'yan takara. Kafin ka yi takara dole sai ka samu goyan bayan kashi 10 cikin 100 na magadan gari da 'yan majalisa. Tun a cikin watan Fabrairu Hukumar Zaben kasa ta soke takarar mutum 17 ciki har da sanannun 'yan adawa irin su Joel Aivo da Reckya Madougou da ta taba rike mukamin minista karkashin tsohon shugaban kasa Boni Yaya, amma tun a farkon watan Maris take tsare bisa zargin tallafa vwa ta'addanci. Wasu 'ya adawa sun yi kaura zuwa Faransa ko Amirka. A kan haka dan takara Corentin Kohoue ya ce dole a kyale 'yan adawa da suka bar kasar su koma gida. Ya ce: "Yanzu ba mai maganar Benin, amma kasa ce da ke zama abar koyi a tsarin dimukuradiyya. Dole ba tare kuma da bata lokaci a bari wadanda suka yi kaura saboda dalilai na siyasa, su dawo gida. Dole a sako firsinonin siyasa. Ya kamata kowa ya shiga a dama da shi a zaben na Benin.

Benin Präsidentschaftswahl
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Ko da yake Benin na da tsayayyen tsarin Dimukuradiyya a Yammacin Afirka da tsarin mulki da ke iya zama abin koyi ga wasu kasashe, amma wasu masana na cewa babu cikakkiyar walwalar siyasa a kasar.