1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Zaben Amurka: Biden ya shiga sahun 'yan Tiktok

February 12, 2024

Shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da amfani da shafin sada zumunta na Tiktok wajen shawo kan galibin matasan da ke amfanin da shafin domin su sake zabarsa a matsayin shugaban kasar a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/4cHqe
Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe BidenHoto: EVELYN HOCKSTEIN/REUTERS

Matakin Shugaba Biden na amfani da Tiktok ya sanya shakku a Washington, kasancewar kamfanin China na ByteDance shi ne ya mallaki Tiktok.

Tun a baya dai 'yan majalisar dokokin Amurka sun sha yin suka kan yadda ake amfani da shafin tare da kira ga hukumomin Amurkan da su dakatar da amfani da Tiktok a kasar, bisa zargin amfani da shi wajen leken asirin al'amuran cikin gidan Amurka daga kasar Sin.

Kamfanin na Tiktok dai ya sha musanta zargin cewa ya na kwarmata bayanan sirrin Amurkan ga Beijing, tare da yin duk mai yiwuwa wajen kare muradun masu amfani da shafin a Amurka.

Hotunan farko a wani 'dan gajeren bidiyo da aka wallafa  na takarar Biden da Kamala sun nuna shugaban ya na amsa tambayoyi daga manema labarai cikin barkwanci kan goyon bayansa ga hukunce-hukuncen jihohin Kansas da San Francisco.

Dandalin Matasa(25-11-21): Matasa da kafofin sada zumunta