1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben Afrika ta Kudu: Zuma ya daukaka kara kan shiga zabe

April 2, 2024

Tsohon shugaban Arfika ta Kudu Jacob Zuma ya daukaka kara kan matakin hukumar zaben kasar na cire sunansa daga cikin jerin 'yan takarar da zasu shiga zaben watan Mayu da za a gudanar a fadin kasar mai cike da cece-kuce.

https://p.dw.com/p/4eMou
Tsohon shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma a yayin zaman kotu a 2021.
Tsohon shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma a yayin zaman kotu a 2021.Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Hukumar zaben kasar Afrika ta Kudu ta ki tantance Mr. Zuma mai shekaru 81, da ke neman takara a wata sabuwar jam'iyya da ya shiga mai suna uMkhonto we Sizwe (MK), bayan raba-gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta ANC mai mulki da kuma batun raina kotu a 2021.

Karin bayani: Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya

Za a gudanar da babban zaben shugaban kasar a watan ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara, da hakan ke kasancewa zabe mafi daukar hankali tun bayan da kasar ta koma kan gwadaben dimukradiyya a 1994.

Karin bayani: Kotu ta sake daure tsohon shugaban Afirka ta Kudu

Shugaba Jacob Zuma da ya mulki kasar ta Afrika ta kudu daga 2009 zuwa 2018, ya gaza komawa kan karagar mulki sakamakon zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa da kuma almubazzaranci da dukiyar kasa.