1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Masar

December 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvIZ

A yau misirawa suka fita kada kuriarsu a zagaye na uku kuma na karshe a zaben yan majalisar dokoki na kasar ta Masar,inda ake sa ran kungiyar Muslim Brotherhood zata samu gagarumin rinjaye, duk kuwa da tsare da yawa daga cikin membobinta da akayi.

An gudanar da zaben ne a larduna guda 9,inda yan takara 1,800 suke takarar kujeru 136.

Tuni dai kungiyar Muslim Brotherhood ta lashe kujeru 76 a zabuka biyu na baya,akwai kuma yiwuwar ta samu kujeru 100 da ake bukata a Majlaisa,r muddin dai rabi daga cikin yan takararta 49 sun samu nasara a wannan zabe.

Wannan ka iya zama wani kalubale ga jamiyar dake mulki ta shugaba Hosni Mubarak wadda dole ne ta ci gaba da rike kashi 2 bisa uku na yawan kujeru na majalisar kafin ta samu rinjaye da ake bukata da zai bata ikon kawo canje canje a kundin tsarin mulkin kasar tare kuma da kafa dokokin gaugawa a kasar.